Skip to content
Ayyukan Manzanni 14:1-7

Ayyukan Manzanni 14:1-7

1
A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.
2
Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa.
3
Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.
4
Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin.
5
Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu.
6
Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,
7
inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options