Skip to content
Ayyukan Manzanni 11:27-30

Ayyukan Manzanni 11:27-30

27
A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima.
28
Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)
29
Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya.
30
Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options