Ayyukan Manzanni 11:22-26
22
Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok.
23
Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.
24
Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.
25
Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu,
26
sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.
Settings