Skip to content
Ayyukan Manzanni 1:16-20

Ayyukan Manzanni 1:16-20

16
ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu
17
dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”
18
(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.
19
Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)
20
Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options