2 Sama’ila 3:6-21
6
Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.
7
To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”
8
Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?
9
Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.
10
Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”
11
Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.
12
Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”
13
Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”
14
Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”
15
Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.
16
Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.
17
Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku.
18
To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’ ”
19
Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.
20
Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.
21
Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.
Settings