Skip to content
2 Sama’ila 3:28-39

2 Sama’ila 3:28-39

28
Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner.
29
Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”
30
(Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)
31
Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.
32
Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.
33
Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?
34
Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.
35
Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”
36
Dukan mutane suka lura suka kuma ji daɗi ƙwarai, tabbatacce kome da sarki ya yi, ya gamshe su.
37
Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner.
38
Sa’an nan sarki ya ce wa mutanensa, “Ba ku gane cewa ɗan sarki kuma babban mutum ya mutu a ƙasar Isra’ila a yau ba?
39
A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options