2 Sama’ila 22:20-30
20
Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
21
“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
22
Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
23
Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
24
Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.
25
Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.
26
“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
27
ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
28
Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
29
Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.
30
Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
Settings