Skip to content
2 Sama’ila 22:31-46

2 Sama’ila 22:31-46

31
“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
32
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
33
Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
34
Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
35
Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
36
Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
37
Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.
38
“Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.
39
Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.
40
Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
41
Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.
42
Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
43
Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.
44
“Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,
45
baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.
46
Zukatansu ta karaya; suka fito da rawan jiki daga kagararsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options