2 Sama’ila 22:19-33
19
Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20
Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
21
“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
22
Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
23
Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
24
Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.
25
Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.
26
“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
27
ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
28
Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
29
Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.
30
Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
31
“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
32
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
33
Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
Settings