Skip to content
2 Sama’ila 20:3

2 Sama’ila 20:3

Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”
2
Saboda haka dukan mutane Isra’ila suka bar Dawuda don su bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka kasance a wurin sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.
3
Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.
4
Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mutanen Yahuda su zo wurina cikin kwana uku, kai kuwa ka kasance a can kai kanka.”
5
Amma da Amasa ya tafi kiran mutanen Yahuda, ya ɗauki lokaci fiye da lokacin da sarki ya ba shi.
6
Dawuda ya ce wa Abishai, “Ina gani Sheba ɗan Bikri zai ba mu wuya fiye da Absalom. Ka ɗauki mutanen maigidanka ka fafare shi, don kada yă sami garuruwa masu katanga yă tsere mana.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options