2 Sama’ila 2:27-32
27
Yowab ya ce, “Muddin Allah yana a raye, da ba a ce ka yi magana ba, da mutanen za su ci gaba da fafaran ’yan’uwansu har gari yă waye.”
28
Sai Yowab ya busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka tsaya; suka daina fafaran Isra’ila. Nan take faɗan ya tsaya.
29
Abner da mutanensa suka ratsa kwarin Urdun dukan dare. Sa’an nan suka haye kogin, suka kuwa ci gaba dukan safe har suka zo Mahanayim.
30
Da Yowab ya dawo daga fafaran Abner, sai ya tattara dukan mutanensa. Ban da Asahel, sai ya gane an rasa mutum goma sha tara na Dawuda.
31
Amma mutanen Dawuda sun kashe mutum ɗari uku da sittin daga kabilar Benyamin da suke tare da Abner.
32
Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.
Settings