2 Sama’ila 12:7-12
7
Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu.
8
Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka.
9
Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa.
10
To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’
11
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka.
12
Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ”
Settings