Skip to content
2 Sama’ila 11:2-5

2 Sama’ila 11:2-5

2
Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai.
3
Sai Dawuda ya aiki wani yă bincika ko wace ce ita, sai mutumin ya dawo ya ce, “Wannan ba Batsheba ba ce, ’yar Eliyam matar Uriya, mutumin Hitti?”
4
Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida.
5
Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options