Skip to content
2 Sama’ila 11:17-27

2 Sama’ila 11:17-27

17
Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.
18
Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.
19
Ya umarci manzon ya ce, “Da ka gama yin wa sarki wannan batun yaƙin,
20
wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba?
21
Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ”
22
Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa.
23
Manzon ya ce wa Dawuda, “Mutanen sun sha kanmu suka fito suka yaƙe mu a fili, amma muka kore su har ƙofar birni.
24
Sa’an nan maharba suka yi ta harbi daga katanga har waɗansu mutanen sarki suka mutu. Ban da haka ma, Uriya mutumin Hitti bawan sarki ya mutu.”
25
Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.”
26
Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi.
27
Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options