2 Bitrus 3:1-4
1
Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau.
2
Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku.
3
Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu.
4
Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”
Settings