Skip to content
2 Bitrus 2:10-22

2 Bitrus 2:10-22

10
Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;
11
duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.
12
Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.
13
Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku.
14
Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!
15
Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.
16
Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.
17
Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.
18
Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.
19
Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.
20
In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko.
21
Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.
22
A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options