Skip to content
2 Sarakuna 6:14-23

2 Sarakuna 6:14-23

14
Sai ya aika da dawakai da kekunan yaƙi da babban rukunin soja zuwa can. Suka bi dare, suka kewaye birnin.
15
Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, “Ranka yă daɗe! Me za mu yi?”
16
Sai annabin ya ce, “Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su.”
17
Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!” Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha.
18
Yayinda abokan gāba suka gangaro wajensa, sai Elisha ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ka sa mutanen nan su zama makafi.” Sai Ubangiji ya buge su da makanta kamar yadda Elisha ya roƙa.
19
Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, zan kuwa kai ku wurin mutumin da kuke nema!” Sai ya kai su Samariya.
20
Bayan suka shiga birnin, sai Elisha ya ce, “Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan don su gani.” Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanunsu suka ga kansu a tsakiyar Samariya.
21
Da sarkin Isra’ila ya gan su, sai ya tambayi Elisha ya ce, “In kashe su ne, mahaifina? In kashe su?”
22
Elisha ya ce, “Kada ka kashe su. Za ka kashe mutanen da ka kame da takobi ko bakanka? Ka ba su abinci da ruwa su ci, su sha, sa’an nan su koma wurin maigidansu.”
23
Saboda haka aka shirya musu babban liyafa, bayan sun ci, suka kuma sha, sai ya tura su zuwa wurin maigidansu. Ta haka ’yan harin Aram suka daina kai hari a yankin Isra’ila.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options