Skip to content
2 Sarakuna 18:28-35

2 Sarakuna 18:28-35

28
Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!
29
Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.
30
Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’
31
“Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,
32
har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’
33
Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?
34
Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna?
35
Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options