2 Sarakuna 10:1-14
1
To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce,
2
“Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,
3
sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”
4
Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”
5
Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”
6
Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.
7
Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
8
Da ɗan saƙon ya iso, sai aka ce wa Yehu, “Sun kawo kawunan ’ya’yan sarki.” Sai Yehu ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar gari har safiya.”
9
Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan?
10
Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.”
11
Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.
12
Sa’an nan Yehu ya nufi Samariya. Da ya kai Bet-Eked na Makiyaya,
13
sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.”
14
Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba.
Settings