Skip to content
2 Korintiyawa 9:12-15

2 Korintiyawa 9:12-15

12
Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.
13
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
14
A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.
15
Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options