- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Baƙin cikin Allah yana kai ga tuba
2 Korintiyawa 7:8-12
8
Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai.
9
Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.
10
Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.
11
Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.
12
To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana.
Settings