2 Korintiyawa 3:12-18
12
Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan.
13
Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa.
14
Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi.
15
Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu.
16
Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin.
17
Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake.
18
Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.
Settings