2 Korintiyawa 2:6-8
6
Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka.
7
Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa.
8
Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.