2 Korintiyawa 2:5-8
5
In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne.
6
Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka.
7
Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa.
8
Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.
Settings