2 Korintiyawa 2:3-4
3
Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.
4
Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.
Settings