2 Korintiyawa 13:5-7
5
Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.
6
Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba.
7
Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings