Skip to content
2 Korintiyawa 13:1-4

2 Korintiyawa 13:1-4

1
Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”
2
Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan,
3
da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
4
Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options