Skip to content
2 Tarihi 36:14-19

2 Tarihi 36:14-19

14
Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.
15
Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.
16
Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.
17
Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.
18
Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.
19
Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options