Skip to content
2 Tarihi 23:1-8

2 Tarihi 23:1-8

1
A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.
2
Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima,
3
dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.
4
Yanzu ga abin da za ku yi, shi ne, kashi ɗaya bisa uku na firistoci da Lawiyawa waɗanda za su yi aiki a Asabbaci su yi tsaro a ƙofofi,
5
kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.
6
Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.
7
Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.”
8
Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options