2 Tarihi 2:1-3
1
Solomon ya ba da umarni don a gina haikali domin sunan Ubangiji da kuma fada wa kansa.
2
Ya ɗebi mutane dubu saba’in su zama ’yan ɗauko, mutane dubu tamanin su zama masu fasa dutse a tuddai, da kuma mutane dubu uku da ɗari shida su zama masu lura da su.
3
Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings