2 Tarihi 16:7-12
7
A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.
8
Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka.
9
Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”
10
Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.
11
Ayyukan mulkin Asa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
12
A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.
Settings