2 Tarihi 14:13-15
13
Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.
14
Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can.
15
Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima.
Settings