1 Timoti 1:3-7
3
Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba
4
ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya.
5
Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.
6
Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana.
7
So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
Settings