1 Sama’ila 2:22-29
22
To, Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin labari duk abin da ’ya’yansa suke yi wa dukan Isra’ila, da yadda suke lalata da matan da suke hidima a bakin ƙofar Tentin Sujada.
23
Saboda haka ya ce musu, “Don me kuke yin waɗannan abubuwa? Na sami labari daga wurin mutane a kan duk ayyukan muguntanku.
24
A’a, ’ya’yana ba labari mai kyau nake ji cikin mutanen Ubangiji ba.
25
In mutum ya yi wa wani laifi Allah yakan kāre shi; amma in mutum ya yi wa Ubangiji zunubi wa zai kāre shi?” Duk da haka, ’ya’yansa ba su kula da gargaɗin mahaifinsu ba, domin nufin Ubangiji ne yă hallaka su.
26
Yaron nan Sama’ila ya dinga girma cikin kwarjini da cikin tagomashi a gaba Ubangiji da mutane.
27
Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?
28
Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.
29
Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’
Settings