1 Sama’ila 2:11-21
11
Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist.
12
’Ya’yan Eli firist, mutane ne masu mugunta. Ba su ɗauki Ubangiji a bakin kome ba.
13
Al’ada ce ga firistoci da mutane cewa in wani ya miƙa hadaya, yayinda nama yake kan wuta, bawan firist zai zo da babban cokali mai yatsu,
14
zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo.
15
Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.”
16
In kuwa mutumin ya ce masa, “Bari kitse yă ƙone tukuna, sa’an nan ka ɗiba duk abin da kake so.” Sai bawan yă ce masa, “A’a, ka ba ni yanzu, in ka ƙi kuwa zan ɗiba ƙarfi da yaji.”
17
Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske.
18
Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin.
19
Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara.
20
Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu ’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida.
21
Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.
Settings