跳到主要内容
1 Sama’ila 18:5-15

1 Sama’ila 18:5-15

5
Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.
6
Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.
7
Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
8
Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”
9
Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.
10
Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.
11
Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.
12
Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.
13
Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su.
14
A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi.
15
Da Shawulu ya ga yadda yake cin nasara, sai ya ji tsoronsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options