1 Bitrus 4:7-11
7
Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.
8
Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
9
Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba.
10
Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.
11
In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.
Settings