Skip to content
1 Sarakuna 10:1-9

1 Sarakuna 10:1-9

1
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.
2
Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta.
3
Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata.
4
Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina.
5
Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai.
6
Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne.
7
Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
8
Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
9
Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options