1 Korintiyawa 5:6-7
6
Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba?
7
Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.