1 Korintiyawa 3:18-20
18
Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima.
19
Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;
20
kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”
Settings