1 Korintiyawa 15:1-8
1
To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai.
2
Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.
3
Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi,
4
cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi,
5
cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun.
6
Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci.
7
Sa’an nan ya bayyana ga Yaƙub, sa’an nan ga dukan manzannin,
8
a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba.
Settings