1 Korintiyawa 12:31
Ana nuna aya 31 tare da mahallin da ke kewaye.
28
A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.
29
Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki?
30
Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara?
31
Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma. Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.
Settings