1 Korintiyawa 12:3-6
3
Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.
4
Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne.
5
Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne.
6
Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
Settings