Skip to content
1 Korintiyawa 12:20-27

1 Korintiyawa 12:20-27

20
Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.
21
Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!”
22
A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci.
23
Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu,
24
gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani,
25
don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna.
26
In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
27
To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options