1 Korintiyawa 12:15-21
15
Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba.
16
Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba.
17
Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?
18
Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama.
19
Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?
20
Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.
21
Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!”
Settings