Skip to content
1 Tarihi 9:35-44

1 Tarihi 9:35-44

35
Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka
36
ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
37
Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot.
38
Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
39
Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
40
Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
41
’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
42
Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
43
Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
44
Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options