1 Tarihi 6:31-38
31
Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
32
Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
33
Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
34
ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,
35
ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,
36
ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
37
ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
38
ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
Settings