Skip to content
1 Tarihi 23:6-23

1 Tarihi 23:6-23

6
Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.
7
Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi.
8
’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.
9
’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.
10
’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.
11
Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.
12
’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.
13
’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.
14
An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.
15
’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer.
16
Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari.
17
Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.
18
’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.
19
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
20
’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu.
21
’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. ’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish.
22
Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.
23
’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options