1 Tarihi 17:11-14
11
sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.
12
Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.
13
Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.
14
Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ”
Settings