1 Tarihi 1:35-54
35
’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora
36
’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek.
37
’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza.
38
’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.
39
’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.
40
’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana.
41
Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
42
’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.
43
Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.
44
Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.
45
Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.
46
Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.
47
Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.
48
Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.
49
Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.
50
Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.
51
Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet
52
Oholibama, Ela, Finon
53
Kenaz, Teman, Mibzar,
54
Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.
Settings